Tirka-tirka ana tara tara. Hujjojin duka an tattara. Lauyoyi sun debi wara. A can kotu kuwa an fara. Tattara hujjoji a fili karara. A cikin kotun koli ba'a bara. In baka da hujja sai ka tara. Wani lokaci ko wata shekara. Wata zai kama, mu dau kara Don tsula biri ya shirya zara. Buri nasa yayi ta kona kara Tsula tuni a kai nasa ya sha gora
Wata ya doso Lokacin tsayawar sa ya taso Jama'a ku zo mu siyo soso Mu wanke dattin kwanso Wata kila tsula zai je gidan kaso Kuma za'a daure **** a kwankwaso Zai yi ta tsalle ko baya so Don ya sha wankan soso
Wai ina yake ne, kantoma Mun sani baka da makoma In ka tafi ba badda kama Duk abin da ka shuka zai girma Zaka girba tabbas ba tantama A gidan kaso ko a magarkama.
An fara duba wata. Ga samaniya ta haskaka Masoyan korra sun rausaya Murna ta su ta wuce zolaya To ina masoya ja? Sun hauhawa. Farashi nasu ya raurawa, ya fadi kasa tamkar wawa. Tun sun ga wata a samaniya, jinjiri me yaye hayaniya, Sun tunzura su yi hayaniya.
Shugaban jam'iyya yace Kowa ya fito da idaniya Ya kura su sama yayi dubiya Jariri na wata zai bayyana A daren yau ko gobe da jibi.