Na gaza yin bacci kuma komai na ci har da abinci na ci amma rayuwa tayi daci saboda dangi na ba bacci A arewaci da kudanci bomabomai sunyi azanci sun rusa kasar limanci saboda tsananin zalunci lallai wannan shine yahudanci sun kama wuri sun ci palasdinawa yayan yanci ku yi hakuri banda takaici duniya ta sai cin hanci kowa so yake sai ya ci ana fakewa da rigar yanci to me ne ne **** yanci a yau ya zama kacici-kacici a tsakanin yan bakin ciki yan yammaci da arewaci har da na gabashi yan kanci