Submit your work, meet writers and drop the ads. Become a member
Safana Jun 2020
Rayuwar ku, ai
Rayuwar mu ce

Rayuwar mu, ai
Rayuwar ku ce

Rayuwar ku rayuwar mu ce
Rayuwar mu rayuwar kuce
Kune sanadin komai
Iyaye kunyi min komai

Bani mantawa
Bani yadawa

Bani yadawa
Bani mantawa

Alkhairin ku ya girma
Ya wuce duk tunani ma
Sanadin rayuwar ku ma
Tawa ta sami alfarma

Bani yada ku
Bani manta ku

Bani manta ku
Bani yada ku

Bani manta koman komai
Tallafin ku ya wuce komai
Faharin ku shine komai
Kune dukkan komai

Ya Mahaifiya ta
Ya Mahaifi na

Ya Mahaifi na
Ya Mahaifiya ta
My parent

Your life, it's
My life

Your life it's our lives
Our lives is your life
You're the reason for everything
And, you did everything

I can't forget...

Thank you
O' Mother
O' Father
Safana Jan 2022
Kallo ya koma can sama
Kowa ya gaza kaiwa sama
Iska a wajen tayi sama
Yaro da kudi yaje sama
Kato ba kudi ya bar sama
Kyawun yan mata ne sama
Saurayi da kudi shine sama
Kai wannan karni ya hau sama
Wai kowa a kasa sai yaje sama
**** ko na saman zai can sama
Burin talakawa su hau sama
Mai kudi haka zai kara sama
Sojan baka zai so yayi sama
Dan siyasar banga, **** ma sama
Yan siyasa, kowa  muje sama
Masu mulki burin su suje sama
Sun manta Allah ne yayi sama
Da abin da yake sama can sama
Ya mallaki komai a cikin sama
Har ikon da yake kasa da sama
In yace komai yayi sama zai sama
In yace kowa yayi sama zai sama
A cikin ikon sa da ke sama
Success is from Allah (God), there must be rich and poor people from the beginning of the life to its end. No one uplifting himself but nature gives him ability to get uplifted as no one gave himself right to live and destiny to dead.

May we be uplifted righteousness without hurting any living thing on this earth.
Safana Feb 2022
Da, da ce
Jiya ma jiya ce
Gobe fa mece ce?
Allah ne zai ce
Yadda yau ita ce
Tayi kyau ta dace
Kamar ace na face
Hanci na ne yace
Na wuce a kaikaice
Kamar naji zan ****
Ta gefena a karkace
Ashe abin karya ce
Wasu sun ce dabi'a ce
Ga yan Adam yaudara ce
Hakikani kaddara ce
Shugabanci, baiwa ce
A baka tama kima ce
Talauci wai musifa ce
An manta komai baiwace
Safana Apr 2024
A wanga kasa ta ke nan
Ba a batun wane sai wancan
Komai iyawar ka baka nan
Tun da ba ka cikin yayan nan

Wanga batu lallai zan farawa
Ba kari ciki balle in yi ragawa
Komai nisan jifa kasa zai fadawa
To ko wane ne jifan zai fadawa

Wani jifan tsami wani ko sai zaki
Kafin a jefa jifan sai an sha yaki
Wani yakin tabbas sai an sa kaki
Na gaba-gaba zai nasara shine sarki

A arewa akwai wani birni shine kebbi
In zaka garin zuru lallai sai ka bi
Birni mai tarihi da yawa an bibbi
Malamai da fatake sun fashewar jalabi
Safana Jun 2024
Akwai sama a cikin sama
A can samaniya Allah ne sama
**** yake komai da ganin dama
**** ne makagin hagu da dama
Rana da wata, ya bar su alama
Mahaliccin halittu da dama
A cikin halittu na sa har da Adama
Daga Adamu ya yi yaya nasa masu kama
Wasu da kiba wasu kuma rama
Tabbas! Tsarki ya tabbata ga mai rahma
Safana Aug 2023
Ku bar mu ta masalaha
Mu ma mu yada fasaha
Komai namu yai araha
Safana Jun 2024
Son ki a jiki na
Ya zarce raina.
Balle ace tunani na
Ya zarce duka gani na.
Da za ace ki kalla
Dubi idanu kalla
Suna Zubar da kwalla
Ina ganin ki talla
Bakin ciki a raina zalla
Dama ki daina talla.

Akan ki ni na manta
Komai a rayuwa ta.
Kaunar ki na jibinta
Dama ki je makaranta
Darasin rayuwa karanta
Tarbiya ki lazumta

Lallai talla yana da riba
Amma ba tallan jiki ba.
Karuwanci ba riba
Zai sa ki shanye taba.
Wata ran ki zama makuba.

Daure ki daina talla
Idanu daina kwalla
Safana Oct 2023
Na gaza yin bacci
kuma komai na ci
har da abinci na ci
amma rayuwa tayi daci
saboda dangi na ba bacci
A arewaci da kudanci
bomabomai sunyi azanci
sun rusa kasar limanci
saboda tsananin zalunci
lallai wannan shine yahudanci
sun kama wuri sun ci
palasdinawa yayan yanci
ku yi hakuri banda takaici
duniya ta sai cin hanci
kowa so yake sai ya ci
ana fakewa da rigar yanci
to me ne ne **** yanci
a yau ya zama kacici-kacici
a tsakanin yan bakin ciki
yan yammaci da arewaci
har da na gabashi yan kanci
Safana Apr 2024
Shekaran jiyan an tattauna
Bayan takardun an kokkona
Duk da majalisar ta zauna
A karshe kowa ya dangana

A kotun farko anyi magana
Ai lallai duka sun tattauna
Tare da lauyoyi sun zauna
An shaida Gawuna ag gwamna

Kuri'un bogi an gano ko ina
Duka hujjojin manya da kana
An gabatar da su da ma'ana
Ga alkalan daukaka kara a bana

Hukunci a bayyane an bayyana
A gaban manya da kanana
Hukuncin daukaka karar a bana
Ya tabbar da Gawuna ne gwamna

Jojin, me sunan kubewa ta miya
Ya ja kaya sai ya dauki aniya
Don bawa karya wata kariya
Don tabbatar da hukuncin karya

Kotu ta zama tamkar fiya-fiya
Alkali ya koma bara da magiya
Domin samin tsotsar kashin miya
Sai ya siyar da iko nasa don dukiya

Ashe ba girin-girin ba tayi mai
Tun da ta leko ta koma ba komai
Kowa sai ya dau dangana kadai
Tabbas wata rana zasu lashe amai
Safana Feb 2023
Na ga al'amari mai yawa
Daga ciki har da na yawa
Masu aikatawa ne wawa
Ba sa yin komai sai wawa
Da kudin masu cin dawa
Nigeria will decide
Safana Oct 2024
Tsantsar Tsananin so
Ya sa na taso
Na yi wankan soso
A zuciya ta kaso kaso.
Ga kauna ta doso.

Da za ki ba ni kyauta
Da sai in kyautata
In kin zamo mata ta
Zan baki kyauta ta

Ki tallafeni ga ni
Komai naki ba ni
In kin kira ni za ni
Na san ki za ki bi ni

Na baki, bani kauna
Sirrin mu kar mu tona
Goben mu za ta nuna
Kaunar mu sai mu auna

— The End —