Submit your work, meet writers and drop the ads. Become a member
Safana Apr 2024
Shekaran jiyan an tattauna
Bayan takardun an kokkona
Duk da majalisar ta zauna
A karshe kowa ya dangana

A kotun farko anyi magana
Ai lallai duka sun tattauna
Tare da lauyoyi sun zauna
An shaida Gawuna ag gwamna

Kuri'un bogi an gano ko ina
Duka hujjojin manya da kana
An gabatar da su da ma'ana
Ga alkalan daukaka kara a bana

Hukunci a bayyane an bayyana
A gaban manya da kanana
Hukuncin daukaka karar a bana
Ya tabbar da Gawuna ne gwamna

Jojin, me sunan kubewa ta miya
Ya ja kaya sai ya dauki aniya
Don bawa karya wata kariya
Don tabbatar da hukuncin karya

Kotu ta zama tamkar fiya-fiya
Alkali ya koma bara da magiya
Domin samin tsotsar kashin miya
Sai ya siyar da iko nasa don dukiya

Ashe ba girin-girin ba tayi mai
Tun da ta leko ta koma ba komai
Kowa sai ya dau dangana kadai
Tabbas wata rana zasu lashe amai
Safana Mar 2021
Ba ra'ayin ka bane
Ba ra'ayi na bane
Ba hange na bane
Ba hangen ka bane
Duniya ba taka bace
Lahira ba' a kauce
Cuta ta nesa ta arce
Ta sa kowa ya fece
Asibitoci an kwace
Kasuwanci ya fauce
Yan makaranta an sace
hancin kowa an face
A gida kowa ya kasance
Miji, yara har ma da mace
Domin nutsuwa kar a fusace
Abubuwa da yawa sun faru a tsakani shekaru kadan, mafi girman su a duniya shine tashin hankalin yaduwar annbobar duniya ta cutar Korona duk da cewa a Nigeria akwai kalubale na shugabanci amma hakan bai hana Al'ummar kasar bin dokokin da aka gindaya musu ba, sai  dai kash! har yanzu akwai shakku dangane da yaduwar cutar a Nigeria ma'ana adadin kididdigar da humkumar NCDC ke fitarwa tun daga farkon fara annobar har izuwa yau akwai alamar tambaya...
Safana Jan 2024
Duk da cewa an tattara
Duk hujjoji a fili karara
lauyoyin  masu kara sun tara
Kishiyoyin su suna ta dara
Duk da sun saka jar dara
A baya sun yi ta bara
Na fada cewa ba a bara
A kotu in an fara
Amma sai da suka yi ta karara
Karshe dai sun yi fara'a

Rashawa da cin hanci sun yi yawa
Har a kotu mai sunan kubewa yayi yawa
Tabbatattun hujjojin ya bawa
Marasa nasara yayan wawa
An kai ruwa rana da yawa
Domin tabbatar da waye wawa
kuma hujjoji sun bayyana wawan
A karshe me sunan kubewa yayi yawa
Michelle A Ford Sep 2020
bing-O
domin-O
hyp-O
psych-O
crypt-O
typ-O

orgasam?


I will never understand our analogy's
#poetichumor #happyfriday #O #selfindulgence #selflove #release

— The End —