Submit your work, meet writers and drop the ads. Become a member
Oct 27
Ina son ki
Ina kaunar ki
...Tamkar ki
Ni banda kamar ki
Ni zan dauke ki
In dora ki a doki

Ke ce hasken haske
Hasken daya haska haske
A zuciya ba wata sai ke
Ga hannu na sai ki rike
A gari sai zancen mu ake
Wai bani da kowa sai ke

Ba wani wai zancen haka ne
Ba ni da kowa tabbas haka ne
Ke ce daya tilo na gane
Kannan ki a guri na kanne ne
Yayyen ki a guri na yayye ne
Kowan ki guri na kowa ne
🎼🎡🎢

Ina son ki
Ina son sunan ki
Inkiyar ki
Da asalin sunan ki
Murmushin ki
Wanda yake kuncin ki
Maganar ki
Ita ce furicin ki
A harshen ki
Har cikin zuciyar ki
Sun dace da siffar ki

Kyakkyawa...
Sunan ki, ga kawa
Ya kan birge kowa
Ke! Har yan adawa
In sun ji suna tafawa

Amintacciya...
Siffar ki, aminiya
Rayuwar ki sam babu hayaniya.

Amina Husnah
Safana
Written by
Safana  27/M
(27/M)   
  161
   Immortality
Please log in to view and add comments on poems