Submit your work, meet writers and drop the ads. Become a member
Oct 2023
Ina kwanan ku yan uwa
nazo gare ku ku ban ruwa
In sha in baiwa yar uwa
lallai na gaza jurewa
rayuwa ta koma yin rawa
kowa ya gaza sai hauhawa
kuma ba'a neman fatawa
sai dai romo na ruwan kawa
in baka da **** sai adawa
in kana dashi sai yin rowa
manya, yara kowa wawa
dan siyasa wai shine giwa
talaka kuwa ai sai dai tsawa
To ku bamu mu ci ko yar dawa
mu zuba mata ko da yar kanwa
mu dafa mu ci mun kore yunwa
Safana
Written by
Safana  27/M
(27/M)   
134
 
Please log in to view and add comments on poems