Ba ra'ayin ka bane Ba ra'ayi na bane Ba hange na bane Ba hangen ka bane Duniya ba taka bace Lahira ba' a kauce Cuta ta nesa ta arce Ta sa kowa ya fece Asibitoci an kwace Kasuwanci ya fauce Yan makaranta an sace hancin kowa an face A gida kowa ya kasance Miji, yara har ma da mace Domin nutsuwa kar a fusace
Abubuwa da yawa sun faru a tsakani shekaru kadan, mafi girman su a duniya shine tashin hankalin yaduwar annbobar duniya ta cutar Korona duk da cewa a Nigeria akwai kalubale na shugabanci amma hakan bai hana Al'ummar kasar bin dokokin da aka gindaya musu ba, sai dai kash! har yanzu akwai shakku dangane da yaduwar cutar a Nigeria ma'ana adadin kididdigar da humkumar NCDC ke fitarwa tun daga farkon fara annobar har izuwa yau akwai alamar tambaya...