Submit your work, meet writers and drop the ads. Become a member
Jan 2021
An share duk wata tantama
Lokacin da babu wata Tama
Da za'a zuba akan tabarma

An fada an nanata fada
Babu fada a tskanin fada
Ta fada tasa na fada a fada

Ga su bature mai jan kunnuwa
Ya kifa hula a ka mara kokuwa
Cak! ya cake kuma ya rike hannuwa

Har da galadima mara hannuwa
Ya dunde kai nasa har kunnuwa
Kai! kace buzu ne a bisaΒ Β ganuwa

An tsare tsari can bisa tsauni
Sai tsala ihu! ni ku sake ni
Ko na dare derere kan tsauni

Kaga gada a gada sai yin dara
Kallo, kifcen gefe ta ankara
Mai harbi da gwafa ta daddara

Ka ji biri da dila yan yaudara
An ajiye kwalba a cike da madara
Sun dauke a guje ba hattara

Kai shaho Sarkin dauka na samaniya
To ka aje ka gudu ka dau anniya
Kar mahari ya hare ka da kibiya
Safana
Written by
Safana  27/M
(27/M)   
930
 
Please log in to view and add comments on poems