Submit your work, meet writers and drop the ads. Become a member
Safana Mar 2024
A kano an murje murja
Gwamna ya mai da murja
Daurawa ya gaza dauriya
Yan kano sun tuna da baba
Ganduje gwani na kowa
Lokacin da ya murje murja
Ba Wanda ya ja da baba
Wasu sun ce wai an juya baba
Lallai, Goggo ce ke juya baban
To yau wa ke juya Abba
Yan kano sun ce "Kilaki"
Ita ce ke juya Gwamnan

Lamarin ya zarce wasa
Hankalin kowa ya Mike
Darajar kowa ta sauka
Ba Wanda ya rage da kima
A kano sai dai su murja
Safana Mar 2024
Murja murza jigida
kin jijjiga jigajigai.
Tsabar iya murji,
Muraja kin jijjiga jigida.
Hmm!
Jigida tasa jigajigai jijjiga.
Daga jin jijjigar jigidar Murja,
jigogi da jigajigai sun jijjiga.
Murja!
A murza mazaunai
sannan a jijjiga jigida.
Tabbas!
Jigogi da jigajiga za su yi
ta jijjiga
Safana Mar 2024
Wai Goggo ke juya na Nagoggo?

E, Goggo ke juya Nagoggon.

To wa ke murza su o' oh?

Ai Murja ke murza murjani,
Murjani ya jijjiga jigida,
Jigidar Murja ta murza su O' oh.
Safana Mar 2024
Murja murza murjani,
Kin iya murji.
Sarauniyar murji
kin iya murji'in taqaliji.
Murja murza mazaunai.
Murja a murzawa Gida-Gida mazaunai.
Murja a zauna a mazauna,
har sai Abida ta koshi da murji.

— The End —