Submit your work, meet writers and drop the ads. Become a member
Safana Jan 2022
Kallo ya koma can sama
Kowa ya gaza kaiwa sama
Iska a wajen tayi sama
Yaro da kudi yaje sama
Kato ba kudi ya bar sama
Kyawun yan mata ne sama
Saurayi da kudi shine sama
Kai wannan karni ya hau sama
Wai kowa a kasa sai yaje sama
**** ko na saman zai can sama
Burin talakawa su hau sama
Mai kudi haka zai kara sama
Sojan baka zai so yayi sama
Dan siyasar banga, **** ma sama
Yan siyasa, kowa  muje sama
Masu mulki burin su suje sama
Sun manta Allah ne yayi sama
Da abin da yake sama can sama
Ya mallaki komai a cikin sama
Har ikon da yake kasa da sama
In yace komai yayi sama zai sama
In yace kowa yayi sama zai sama
A cikin ikon sa da ke sama
Success is from Allah (God), there must be rich and poor people from the beginning of the life to its end. No one uplifting himself but nature gives him ability to get uplifted as no one gave himself right to live and destiny to dead.

May we be uplifted righteousness without hurting any living thing on this earth.
Safana Oct 2024
Ina son ki
Ina kaunar ki
...Tamkar ki
Ni banda kamar ki
Ni zan dauke ki
In dora ki a doki

Ke ce hasken haske
Hasken daya haska haske
A zuciya ba wata sai ke
Ga hannu na sai ki rike
A gari sai zancen mu ake
Wai bani da kowa sai ke

Ba wani wai zancen haka ne
Ba ni da kowa tabbas haka ne
Ke ce daya tilo na gane
Kannan ki a guri na kanne ne
Yayyen ki a guri na yayye ne
Kowan ki guri na kowa ne
🎼🎵🎶

Ina son ki
Ina son sunan ki
Inkiyar ki
Da asalin sunan ki
Murmushin ki
Wanda yake kuncin ki
Maganar ki
Ita ce furicin ki
A harshen ki
Har cikin zuciyar ki
Sun dace da siffar ki

Kyakkyawa...
Sunan ki, ga kawa
Ya kan birge kowa
Ke! Har yan adawa
In sun ji suna tafawa

Amintacciya...
Siffar ki, aminiya
Rayuwar ki sam babu hayaniya.

Amina Husnah
Safana Nov 2022
Akwai wani mutum da baya karya
A cikin al'amuransa baya karaya
A kowanne yanayi baya kada garaya
A duk wahala baya juya baya
A yanayin fushi baya jayayya
A cikin daji ya kan dauki kaya


Bashi da yaudara ko kifadi
Baya tsoron ta kife in ya fadi
Baya ja da baya wajen tadi
Baya tsoro ko da za'ayi shadi
Baya rowa wajen bada madi
Baya taka rawa duk dadin kidi


Cikakken adali ne **** kowa yabi
Cikin jama'a kuwa baya harbi
Cincirundon jama'a sunyi masa lakabi
Farar aniya laya sai muyi ta bi
Saboda yaja raganar kowa sai muyi tabi
Tafi-tafi dai GAWUNA kowa ya bi
Safana Mar 2024
A kano an murje murja
Gwamna ya mai da murja
Daurawa ya gaza dauriya
Yan kano sun tuna da baba
Ganduje gwani na kowa
Lokacin da ya murje murja
Ba Wanda ya ja da baba
Wasu sun ce wai an juya baba
Lallai, Goggo ce ke juya baban
To yau wa ke juya Abba
Yan kano sun ce "Kilaki"
Ita ce ke juya Gwamnan

Lamarin ya zarce wasa
Hankalin kowa ya Mike
Darajar kowa ta sauka
Ba Wanda ya rage da kima
A kano sai dai su murja
Safana Mar 2021
Ba ra'ayin ka bane
Ba ra'ayi na bane
Ba hange na bane
Ba hangen ka bane
Duniya ba taka bace
Lahira ba' a kauce
Cuta ta nesa ta arce
Ta sa kowa ya fece
Asibitoci an kwace
Kasuwanci ya fauce
Yan makaranta an sace
hancin kowa an face
A gida kowa ya kasance
Miji, yara har ma da mace
Domin nutsuwa kar a fusace
Abubuwa da yawa sun faru a tsakani shekaru kadan, mafi girman su a duniya shine tashin hankalin yaduwar annbobar duniya ta cutar Korona duk da cewa a Nigeria akwai kalubale na shugabanci amma hakan bai hana Al'ummar kasar bin dokokin da aka gindaya musu ba, sai  dai kash! har yanzu akwai shakku dangane da yaduwar cutar a Nigeria ma'ana adadin kididdigar da humkumar NCDC ke fitarwa tun daga farkon fara annobar har izuwa yau akwai alamar tambaya...
Safana Jan 2023
Na fada muku gaskiya
kowa sai ya dau aniya
Don gyara hayaniya
sai mu dandana jar miya
babu sauran magiya
ko mu dandana farar fiya
amma banda fariya
tun da mun kife rariya

waye zaya zagaya
ya riko mana ragaya
sai dai kai kai daya
Tinubun mu guda daya
wanda **** zai waiwaya
yan baya su sha miya
babu mai tako kaya
ko ya dauko duniya

Wai a kasar mu gaba daya
wa ne ne mai aniya
ta jan ragama daya
to ku amsa gaba daya
Tinubun mu **** daya

wa ne ne mai juriya
ta rike nijeriya
Tinubun mu **** **** daya

wa ne ne a tsakiya
wanda kowa na bibiya
Na ce Tinubu ne guda daya

wa ye zai yafiya
yafiyar yan mamaya
Tinubu ne **** daya
Babu bambancin kabila, a matsayina na Bahaushe, yafi na zabi Bayerabe domin yana da abubuwa da yawa da zai kawo wa kasar ta mu Najeriya. Hangen sa yana da fadi, kuma manufarsa tana da ƙarfi.
Safana Nov 2023
(ALHAJI (DR.) AMINU ADO BAYERO)
Kakkaki
Bidigar Sarki

Jama'ar birni ku fito...
Makasau Dan Bakan Dabo Ya fito.

Makasau Sarkin Kano Ya fito
Dan Bakan Dabo, Sarki ya fito
Aminu Ado, sai da kayi ya fito
Saki a kano mai tumbe ya fito

Jikan Dabo me ado dan bakan Dabo
Makasau sarkin kano mai adon Dabo
Me kyautar nera da anini da da kwabo
A tarihi nasa an duba kaf babu tabo
Ya mike ya tafi al'uma suna ta Odabo

Tgwayen sarkin Bichi da kano
Fata nasa kowa ya ci a kwano
Talawansa su mori dandano
Na mulki nasa a ***** da Kano
Tare da **** a kyakkyawan kwano

Jikan Bayero sam baka da raini
A cikin dami da sanyi ko ko a rani
Jama'a na kaunar ka fanni fanni
Saboda kautar nera da anini
Da jin kai ga talakawan ka a birni

Kirkin ka ya zagawa birni da kauye
Ta ko ina alherin ka ya mamaye
Gwani, Idan kayi alheri baka waiwaye
Saboda a cikin alheri kake a zagaye
Hm! makiyan ka kullum za su karairaye

Mai hakuri dan mai hakuri, Makasau
Ka jure hawan Sallah har zuwa fanisau
Akan ingarman dikin ka kamar kosau
Wanda babu irin sa ko an je misau

Muhammadu Aminu dan Ado Bayero
Garnakaki namiji a kyuatar ka ba zero
Tsabar ilimin ka turawan sun baka biro
Cacnselo a calaba ka wuce a ce Pro
Sharrin makiyan k ba ya zuwa ko sun huro

dan Bakan Dabo jikan dabo me jalla
In ka fito, kwalliyar ka kowa sai ya kalla
ana rububin alaka da kai sai an kulla
Amma su wancanan ka sai anyi talla
Kai! a kano kai kadai ne sarki zalla

Kai ka yi kama da Bakan Dabo Ado
Mai martaba marigayi sarkin ado
Tabbas wannan haka yake kayo gado
Tun da ka dare karagar mulkin ka na gado
hakika makiyan ka ko sun bi sai sun gudo

Ina me ja ya zo ga me tsinkawa
Wani ya taba ja mun kai **** takalmawa
sai da yayi tattaki ya bi ta wudilawa
Ya rtsa gonaki yabi ketaren farawa
gashi ta maimaita carki ya tafi ba dwowa

Makasau ginshiki ne ga kano da kanawa
makasau dirka ne ga kano ba karyewa
Makasau Uba ne ga kano ba sauyawa
Makasau ka gaji bakan dabo babu adawa
Makasau ne sarki daya a kani anyi yabawa
Safana Oct 2023
Ina kwanan ku yan uwa
nazo gare ku ku ban ruwa
In sha in baiwa yar uwa
lallai na gaza jurewa
rayuwa ta koma yin rawa
kowa ya gaza sai hauhawa
kuma ba'a neman fatawa
sai dai romo na ruwan kawa
in baka da **** sai adawa
in kana dashi sai yin rowa
manya, yara kowa wawa
dan siyasa wai shine giwa
talaka kuwa ai sai dai tsawa
To ku bamu mu ci ko yar dawa
mu zuba mata ko da yar kanwa
mu dafa mu ci mun kore yunwa
Safana Apr 2024
Shekaran jiyan an tattauna
Bayan takardun an kokkona
Duk da majalisar ta zauna
A karshe kowa ya dangana

A kotun farko anyi magana
Ai lallai duka sun tattauna
Tare da lauyoyi sun zauna
An shaida Gawuna ag gwamna

Kuri'un bogi an gano ko ina
Duka hujjojin manya da kana
An gabatar da su da ma'ana
Ga alkalan daukaka kara a bana

Hukunci a bayyane an bayyana
A gaban manya da kanana
Hukuncin daukaka karar a bana
Ya tabbar da Gawuna ne gwamna

Jojin, me sunan kubewa ta miya
Ya ja kaya sai ya dauki aniya
Don bawa karya wata kariya
Don tabbatar da hukuncin karya

Kotu ta zama tamkar fiya-fiya
Alkali ya koma bara da magiya
Domin samin tsotsar kashin miya
Sai ya siyar da iko nasa don dukiya

Ashe ba girin-girin ba tayi mai
Tun da ta leko ta koma ba komai
Kowa sai ya dau dangana kadai
Tabbas wata rana zasu lashe amai
Safana Apr 2022
G = Gwani na gwanaye Gwamnan gobe
A = A Gurin jama' a gwani kai  ne zobe
W= Waliyin Gwamna a Kano ko ba zabe
U = Uban marasa gata mai yi musu dabe
N = Nasiru Dan Yusif ne ka gagara dambe
A = A kano kowa ya bi don ka wuce Rabe
Safana Jan 2024
Tirka-tirka ana tara tara.
Hujjojin duka an tattara.
Lauyoyi sun debi wara.
A can kotu kuwa an fara.
Tattara hujjoji a fili karara.
A cikin kotun koli ba'a bara.
In baka da hujja sai ka tara.
Wani lokaci ko wata shekara.
Wata zai kama, mu dau kara
Don tsula biri ya shirya zara.
Buri nasa yayi ta kona kara
Tsula tuni a kai nasa ya sha gora

Wata ya doso
Lokacin tsayawar sa ya taso
Jama'a ku zo mu siyo soso
Mu wanke dattin kwanso
Wata kila tsula zai je gidan kaso
Kuma za'a daure **** a kwankwaso
Zai yi ta tsalle ko baya so
Don ya sha wankan soso

Wai ina yake ne, kantoma
Mun sani baka da makoma
In  ka tafi ba badda kama
Duk abin da ka shuka zai girma
Zaka girba tabbas ba tantama
A gidan kaso ko a magarkama.

An fara duba wata.
Ga samaniya ta haskaka
Masoyan korra sun rausaya
Murna ta su ta wuce zolaya
To ina masoya ja?
Sun hauhawa.
Farashi nasu ya raurawa,
ya fadi kasa tamkar wawa.
Tun sun ga wata a samaniya,
jinjiri me yaye hayaniya,
Sun tunzura su yi hayaniya.

Shugaban jam'iyya yace
Kowa ya fito da idaniya
Ya kura su sama yayi dubiya
Jariri na wata zai bayyana
A daren yau ko gobe da jibi.
Safana Jul 2023
Matakin nasara hakuri.
matakin mutuwa kakari.
Matakin tauna hakori.
abin yin faskare ne gatari.
Kowa yana gudun hatsari.
Uwa da yaya sai bari bari.
Mara wanka kullum sai kari.
A cinye gona sai fari.
Yabanya Allah ya fishheki fari.
Safana Oct 2023
Babu riba babu rabo
rayuwa sai anyi rabo
kowa ya samu ya ta6o
idan kana da kwabo
sai kayi ta odabo
idan baka da **** ka kar6o
ka siyo wa dan ka ko da bobo
Safana Oct 2023
Na gaza yin bacci
kuma komai na ci
har da abinci na ci
amma rayuwa tayi daci
saboda dangi na ba bacci
A arewaci da kudanci
bomabomai sunyi azanci
sun rusa kasar limanci
saboda tsananin zalunci
lallai wannan shine yahudanci
sun kama wuri sun ci
palasdinawa yayan yanci
ku yi hakuri banda takaici
duniya ta sai cin hanci
kowa so yake sai ya ci
ana fakewa da rigar yanci
to me ne ne **** yanci
a yau ya zama kacici-kacici
a tsakanin yan bakin ciki
yan yammaci da arewaci
har da na gabashi yan kanci
Safana Mar 2022
Rasha, wuta ce a duniya
Zafi nata yafi na Arabiya
Ta sa yara kuka a samaniya
A cikin su har da su jojiya
Tun talatali har da ceceniya
Rana tsaka tabi yukreniya
Ta share fage da sakaliya
Kowa tsoro sai hayaniya
Ya kasa kata6us sai kiriniya
Ya kasa zuwa farfajiya
Ya kasa ya tsare ayi rakiya
Safana Sep 2020
Alkalamin bazai bushe ba
Tsoro! ba dan Bahaushe ba
Naman dai baza a gashe ba
Kowace miya badai taushe ba
Dukka kudin baza a kashe ba
Shukoki ba sai na dashe ba
Kowa ne bam baza ya fashe ba
Kokonton mata kaji sun ce, Ashe ba!
Hausa ba dabo
Safana Apr 2024
Bissimillahi da Allah zan kago.
Mahaliccin kowa wanda ya kago.
Saiwa a kasa tamkar rogo.
In ya fiddo ka ba me saka a kogo.
A cikin tafiya lallai zan bi a zango.
Na ayari kuma mu ya da zango.
A cikin tafiyar har da Adamu Zango.
Me kamar zaki don ya wuce rago
Ba ya kyautar yadi sai naman rago.
Kyautar sa, sai Azurfa har da agogo.
Yana bawa makiyan sa, gajere har dogo.
Ya kan lullabe  su da dadi har bargo.
Lakabi nasa Dan Gayu me hannun ungo.

**** me hakuri mawadaci ne tun farko.
Duk tsanani ba a dana masa tarko.
Ko an dana masa sai yayi karko.
Mahassada nasa sai shan katako.
Safe da rana zai ta zuba musu koko.
Suna daukar masa kaya, Hm! Yan dako.
A cikin zafi da sanyi da ruwa mamako.
Adam Zango me gari
Yaro ne adon gari
Safana Apr 2024
Mun yi ado kowa ya kallah.
Mun dau hanyar filin sallah.
Muna tasbihi dallah dallah.
Muna cewa karba mana Ya Allah.
Muna cewa amsa mana Ya Allah.
Muna cewa yafe mana Ya Allah.
Muna cewa datar da mu Ya Allah.
A ranar idin karamar sallah
Eid-al-fitr

— The End —