Submit your work, meet writers and drop the ads. Become a member
Ahmad Almustapha Jun 2021
Bauchi naman-keya, ga kitse ga tauri

Bauchi kaya bakusan nagida ba, ku keta rigan yaro ku keta rigan baba

Bauchi talala mai kamar sake, ta nesa mekamar akama amma kuma tai-nisa

Baku son kudi sai iko, ana ganinku wawaye, kuna ganin su sune wawa

Gabaruwa mejima ta Malam Yakubu, meson yini zai kwana, mai kwana zaiyi wata, me wata zai shekara, daga shekara ka zauna dabas, garin karo kuma garin harga Allah Dada

Yaro kaso fada kwari ya kare, garin kaso mutun karasa abin bashi, garu gara da naka in babu naka kare yafika
Bauchi biwai namijin gari
Safana May 2020
Zuciya ta tayi kamar zuma
Kai zaki nata ya wuce ai zuma
Na dauka akai zani garin Zuma...
Na Abuja da Niger garin su Fatima
Safana Apr 2024
A wanga kasa ta ke nan
Ba a batun wane sai wancan
Komai iyawar ka baka nan
Tun da ba ka cikin yayan nan

Wanga batu lallai zan farawa
Ba kari ciki balle in yi ragawa
Komai nisan jifa kasa zai fadawa
To ko wane ne jifan zai fadawa

Wani jifan tsami wani ko sai zaki
Kafin a jefa jifan sai an sha yaki
Wani yakin tabbas sai an sa kaki
Na gaba-gaba zai nasara shine sarki

A arewa akwai wani birni shine kebbi
In zaka garin zuru lallai sai ka bi
Birni mai tarihi da yawa an bibbi
Malamai da fatake sun fashewar jalabi

— The End —