Submit your work, meet writers and drop the ads. Become a member
Safana Apr 2022
Saudatu yan mata
Ki yi mini tatata
Sai ki zamo mata ta
A guri na ke ce yar gata

Na fara da ke cikin raina
Ni ban san ki ba a ko ina
Gashi na fada a labari na
Saudatu yan mata ce, burina

Nayi gamo da so, boyayye
Har a cikin raina, ya baibaye
A cikin zuciya ya kanainaye
Ya cike gurbin can da na boye

Nayi nutso cikin tafkin Soyayya
Na rasa kaina cikin kokon zuciya
Dama zaki bani yarda a samaniya
Da na zama sarki ke ko sarauniya

Saudatu yan mata
Karbi bukata ta
Ki mini tatata
Ki zamo mata ta
Safana Jan 2022
Kallo ya koma can sama
Kowa ya gaza kaiwa sama
Iska a wajen tayi sama
Yaro da kudi yaje sama
Kato ba kudi ya bar sama
Kyawun yan mata ne sama
Saurayi da kudi shine sama
Kai wannan karni ya hau sama
Wai kowa a kasa sai yaje sama
**** ko na saman zai can sama
Burin talakawa su hau sama
Mai kudi haka zai kara sama
Sojan baka zai so yayi sama
Dan siyasar banga, **** ma sama
Yan siyasa, kowa  muje sama
Masu mulki burin su suje sama
Sun manta Allah ne yayi sama
Da abin da yake sama can sama
Ya mallaki komai a cikin sama
Har ikon da yake kasa da sama
In yace komai yayi sama zai sama
In yace kowa yayi sama zai sama
A cikin ikon sa da ke sama
Success is from Allah (God), there must be rich and poor people from the beginning of the life to its end. No one uplifting himself but nature gives him ability to get uplifted as no one gave himself right to live and destiny to dead.

May we be uplifted righteousness without hurting any living thing on this earth.
Safana Nov 2022
Akwai wani mutum da baya karya
A cikin al'amuransa baya karaya
A kowanne yanayi baya kada garaya
A duk wahala baya juya baya
A yanayin fushi baya jayayya
A cikin daji ya kan dauki kaya


Bashi da yaudara ko kifadi
Baya tsoron ta kife in ya fadi
Baya ja da baya wajen tadi
Baya tsoro ko da za'ayi shadi
Baya rowa wajen bada madi
Baya taka rawa duk dadin kidi


Cikakken adali ne **** kowa yabi
Cikin jama'a kuwa baya harbi
Cincirundon jama'a sunyi masa lakabi
Farar aniya laya sai muyi ta bi
Saboda yaja raganar kowa sai muyi tabi
Tafi-tafi dai GAWUNA kowa ya bi
Safana Apr 2024
Bissimillahi da Allah zan kago.
Mahaliccin kowa wanda ya kago.
Saiwa a kasa tamkar rogo.
In ya fiddo ka ba me saka a kogo.
A cikin tafiya lallai zan bi a zango.
Na ayari kuma mu ya da zango.
A cikin tafiyar har da Adamu Zango.
Me kamar zaki don ya wuce rago
Ba ya kyautar yadi sai naman rago.
Kyautar sa, sai Azurfa har da agogo.
Yana bawa makiyan sa, gajere har dogo.
Ya kan lullabe  su da dadi har bargo.
Lakabi nasa Dan Gayu me hannun ungo.

**** me hakuri mawadaci ne tun farko.
Duk tsanani ba a dana masa tarko.
Ko an dana masa sai yayi karko.
Mahassada nasa sai shan katako.
Safe da rana zai ta zuba musu koko.
Suna daukar masa kaya, Hm! Yan dako.
A cikin zafi da sanyi da ruwa mamako.
Adam Zango me gari
Yaro ne adon gari
Safana Nov 2023
(ALHAJI (DR.) AMINU ADO BAYERO)
Kakkaki
Bidigar Sarki

Jama'ar birni ku fito...
Makasau Dan Bakan Dabo Ya fito.

Makasau Sarkin Kano Ya fito
Dan Bakan Dabo, Sarki ya fito
Aminu Ado, sai da kayi ya fito
Saki a kano mai tumbe ya fito

Jikan Dabo me ado dan bakan Dabo
Makasau sarkin kano mai adon Dabo
Me kyautar nera da anini da da kwabo
A tarihi nasa an duba kaf babu tabo
Ya mike ya tafi al'uma suna ta Odabo

Tgwayen sarkin Bichi da kano
Fata nasa kowa ya ci a kwano
Talawansa su mori dandano
Na mulki nasa a ***** da Kano
Tare da **** a kyakkyawan kwano

Jikan Bayero sam baka da raini
A cikin dami da sanyi ko ko a rani
Jama'a na kaunar ka fanni fanni
Saboda kautar nera da anini
Da jin kai ga talakawan ka a birni

Kirkin ka ya zagawa birni da kauye
Ta ko ina alherin ka ya mamaye
Gwani, Idan kayi alheri baka waiwaye
Saboda a cikin alheri kake a zagaye
Hm! makiyan ka kullum za su karairaye

Mai hakuri dan mai hakuri, Makasau
Ka jure hawan Sallah har zuwa fanisau
Akan ingarman dikin ka kamar kosau
Wanda babu irin sa ko an je misau

Muhammadu Aminu dan Ado Bayero
Garnakaki namiji a kyuatar ka ba zero
Tsabar ilimin ka turawan sun baka biro
Cacnselo a calaba ka wuce a ce Pro
Sharrin makiyan k ba ya zuwa ko sun huro

dan Bakan Dabo jikan dabo me jalla
In ka fito, kwalliyar ka kowa sai ya kalla
ana rububin alaka da kai sai an kulla
Amma su wancanan ka sai anyi talla
Kai! a kano kai kadai ne sarki zalla

Kai ka yi kama da Bakan Dabo Ado
Mai martaba marigayi sarkin ado
Tabbas wannan haka yake kayo gado
Tun da ka dare karagar mulkin ka na gado
hakika makiyan ka ko sun bi sai sun gudo

Ina me ja ya zo ga me tsinkawa
Wani ya taba ja mun kai **** takalmawa
sai da yayi tattaki ya bi ta wudilawa
Ya rtsa gonaki yabi ketaren farawa
gashi ta maimaita carki ya tafi ba dwowa

Makasau ginshiki ne ga kano da kanawa
makasau dirka ne ga kano ba karyewa
Makasau Uba ne ga kano ba sauyawa
Makasau ka gaji bakan dabo babu adawa
Makasau ne sarki daya a kani anyi yabawa
Safana Jun 2024
Akwai sama a cikin sama
A can samaniya Allah ne sama
**** yake komai da ganin dama
**** ne makagin hagu da dama
Rana da wata, ya bar su alama
Mahaliccin halittu da dama
A cikin halittu na sa har da Adama
Daga Adamu ya yi yaya nasa masu kama
Wasu da kiba wasu kuma rama
Tabbas! Tsarki ya tabbata ga mai rahma
Safana Jan 2024
Tirka-tirka ana tara tara.
Hujjojin duka an tattara.
Lauyoyi sun debi wara.
A can kotu kuwa an fara.
Tattara hujjoji a fili karara.
A cikin kotun koli ba'a bara.
In baka da hujja sai ka tara.
Wani lokaci ko wata shekara.
Wata zai kama, mu dau kara
Don tsula biri ya shirya zara.
Buri nasa yayi ta kona kara
Tsula tuni a kai nasa ya sha gora

Wata ya doso
Lokacin tsayawar sa ya taso
Jama'a ku zo mu siyo soso
Mu wanke dattin kwanso
Wata kila tsula zai je gidan kaso
Kuma za'a daure **** a kwankwaso
Zai yi ta tsalle ko baya so
Don ya sha wankan soso

Wai ina yake ne, kantoma
Mun sani baka da makoma
In  ka tafi ba badda kama
Duk abin da ka shuka zai girma
Zaka girba tabbas ba tantama
A gidan kaso ko a magarkama.

An fara duba wata.
Ga samaniya ta haskaka
Masoyan korra sun rausaya
Murna ta su ta wuce zolaya
To ina masoya ja?
Sun hauhawa.
Farashi nasu ya raurawa,
ya fadi kasa tamkar wawa.
Tun sun ga wata a samaniya,
jinjiri me yaye hayaniya,
Sun tunzura su yi hayaniya.

Shugaban jam'iyya yace
Kowa ya fito da idaniya
Ya kura su sama yayi dubiya
Jariri na wata zai bayyana
A daren yau ko gobe da jibi.
Safana Apr 2022
Ka mike an ce karkata
Kai!  taka an ce tatata
Yaushe ne rana za ta?
Gani na abokin ta wata
Ba rana, sati har wata
Tun da na hango yar wata
Mata daga gefe na kai mata
Hari dan na nuna bajinta ta
Ai ko sai tayi mini raf ta ta
Ta rike hannu na me kanta
Sai ta ja ni cikin dangi na ta
Tai ta nuni ga dangi nan na ta
Baba yayi murna babu karkata
Umma ta taka yar rawa ta ta
Don murna har da kawa ta ta
Maganar  aure ce na yi mata
Tun da fari ta dauke kai nata
Ta bi son rai da kawaye nata
Mai kudi shine a gaba nata
Na manta har da batu na ta
Rana daya sai ga kira na ta

Gaisuwa ta Mahaifi na tayi
Ra'ayi, sauyawa ta sa na yi
Tausayi shine da yasa nayi
Kan batun labarin da tayi
Zuciya ta raurawa nan tayi
Tausayawa zuciya ta nan tayi
Na amshi batun ta kuma za'ayi
Takure kai na duka ni nayi
Do na nuna bajinta da ra'ayi
Na kudurce aure ne zamu yi
Yan uwa murna duka sun tayi
Fatan alheri an ta yi
Na ganin auren mu da za'ayi
Gashi nan dai auren an yi
Tun da fari fa zaki ne yayi
Dandanon madara duka yayi
Har Zuma da madi duka yayi
Daga baya ta sauya ra'ayi

Na shiga uku na kara uku
Bana son na shige can kurkuku
In na kara shiga uku sau uku
Safana Mar 2022
Na riko wanni abu
Can cikin zuciya babu mai sa janye
Don ko shine gaba na

Zuciya ta rkice...
Tun daren da na ganka
Zuciya ta kagauta kai nake so na gani

Ya ka dan saurayi
Kai nake so ka gane
Ba bu mai sa ni na janye duk kalamai da nai

Hankali na
Zuciya ta
Dukka sun  kagauta
So nake yi na ganka
Ka zamo kussa da ni

Kai Habeeb dan Habeeb
So da kauna na ba ka
Ba bu mai sa na karbe
Don ko kai ne a gaba

Auwal ne
Auwal ne
Auwal ne

Auwal ka gane
Son ka ya mamaye
Zuciya ta da raina
Rayuwa ta ka ce

In kano so
Sai ka so
Dukka ni ta ka ce

Auwal ne
Auwal ne
Auwal ne
Safana Oct 2024
Ina son ki
Ina kaunar ki
...Tamkar ki
Ni banda kamar ki
Ni zan dauke ki
In dora ki a doki

Ke ce hasken haske
Hasken daya haska haske
A zuciya ba wata sai ke
Ga hannu na sai ki rike
A gari sai zancen mu ake
Wai bani da kowa sai ke

Ba wani wai zancen haka ne
Ba ni da kowa tabbas haka ne
Ke ce daya tilo na gane
Kannan ki a guri na kanne ne
Yayyen ki a guri na yayye ne
Kowan ki guri na kowa ne
🎼🎵🎶

Ina son ki
Ina son sunan ki
Inkiyar ki
Da asalin sunan ki
Murmushin ki
Wanda yake kuncin ki
Maganar ki
Ita ce furicin ki
A harshen ki
Har cikin zuciyar ki
Sun dace da siffar ki

Kyakkyawa...
Sunan ki, ga kawa
Ya kan birge kowa
Ke! Har yan adawa
In sun ji suna tafawa

Amintacciya...
Siffar ki, aminiya
Rayuwar ki sam babu hayaniya.

Amina Husnah
Safana Apr 2021
In Allah ya yarda
za mu yi aure...
Mu zauna tare...
Dukka hakkokin ki
ni zani kare...
Mu yo rayuwa
bamu ware...
Dukka dangi na
naki ne babu bare...
Zamu zauna a tare...
Zani so ki haifa mini
jinjiraye yan farare...

Rayuwa tana kamshi
idan an zauna da mai
turare...
Ko a kauye zaka ga yara
da safe, sun dauko karare...
Mata kuwa, a gona tare...
suna daukar kirare...
Ga iskar damuna tana
kadawa har da fure farare...
Korama mai sanyin yashi
ruwa ya ketare...
Ga mu cikin lambu
ni da ke mun tattare...
Dukka kayan lambu a
gaban mu, mun ciccire...

Haka ne...

In Allah ya yarda
Za mu yi Aure...

In Allah ya yarda
Za mu yi Aure...

In Allah ya yarda
Za mu yi Aure...
Safana Mar 2022
Safana gari ne...
Safana gari ne...
Safana gari ne...

Safana gari ne
Na tabbata zan kwana cikin sa
Ba bu yadda za ai na barshi don
Ya zamo mahalli na...
Safana Feb 2022
Kukan kucciya ya bi ciyawa
Gero, maiwa sun fi su dawa
Matan yanzu sun fiya kawa
Mai ilmi sam bai da adawa
Danben mata ya fi ga kokawa
Daci, yaji kai har da su kanwa
Zaka gani mata sun rarrawa
In suka lasa sai kaga yar rawa
Mata, manya mata ne da alewa
Zaki ne a cikin su yafi alewa
Waye  zaya ki lasa sai wawa
Na hada Sarki kai har fadawa
Siriri, Kato har dan kokawa
Na fada na kuma maimaitawa
Safana Mar 2022
Rasha, wuta ce a duniya
Zafi nata yafi na Arabiya
Ta sa yara kuka a samaniya
A cikin su har da su jojiya
Tun talatali har da ceceniya
Rana tsaka tabi yukreniya
Ta share fage da sakaliya
Kowa tsoro sai hayaniya
Ya kasa kata6us sai kiriniya
Ya kasa zuwa farfajiya
Ya kasa ya tsare ayi rakiya
Safana Mar 2022
A cikin daji...
Dan Fulani a jeji
Inda babu ko aji
Balle kukan kaji
Yayi guzurin yaji
Zai ci kosai da yaji
Safana Dec 2020
Bahaushe kan ce bakin ciki
yayin da wani abu a can ciki
Ko lokacin daci a wajen ciki
ko da hassada a cikin ciki
Bakin ciki babu kyu
Safana Apr 2024
A wanga kasa ta ke nan
Ba a batun wane sai wancan
Komai iyawar ka baka nan
Tun da ba ka cikin yayan nan

Wanga batu lallai zan farawa
Ba kari ciki balle in yi ragawa
Komai nisan jifa kasa zai fadawa
To ko wane ne jifan zai fadawa

Wani jifan tsami wani ko sai zaki
Kafin a jefa jifan sai an sha yaki
Wani yakin tabbas sai an sa kaki
Na gaba-gaba zai nasara shine sarki

A arewa akwai wani birni shine kebbi
In zaka garin zuru lallai sai ka bi
Birni mai tarihi da yawa an bibbi
Malamai da fatake sun fashewar jalabi

— The End —