Submit your work, meet writers and drop the ads. Become a member
Safana Dec 2020
Bahaushe kan ce bakin ciki
yayin da wani abu a can ciki
Ko lokacin daci a wajen ciki
ko da hassada a cikin ciki
Bakin ciki babu kyu
Safana Sep 2021
Carol tayi sauri
ta zo ta kula mu
ta saka bakunan mu
su furta ciki na ran mu
Abin da yake a ran mu
fuskar mu fari ta kamu
da hasken rana akan mu
Carol tayi sauri
Hausa rhyme for carol
Safana Jun 2024
Son ki a jiki na
Ya zarce raina.
Balle ace tunani na
Ya zarce duka gani na.
Da za ace ki kalla
Dubi idanu kalla
Suna Zubar da kwalla
Ina ganin ki talla
Bakin ciki a raina zalla
Dama ki daina talla.

Akan ki ni na manta
Komai a rayuwa ta.
Kaunar ki na jibinta
Dama ki je makaranta
Darasin rayuwa karanta
Tarbiya ki lazumta

Lallai talla yana da riba
Amma ba tallan jiki ba.
Karuwanci ba riba
Zai sa ki shanye taba.
Wata ran ki zama makuba.

Daure ki daina talla
Idanu daina kwalla
Safana Oct 2023
Na gaza yin bacci
kuma komai na ci
har da abinci na ci
amma rayuwa tayi daci
saboda dangi na ba bacci
A arewaci da kudanci
bomabomai sunyi azanci
sun rusa kasar limanci
saboda tsananin zalunci
lallai wannan shine yahudanci
sun kama wuri sun ci
palasdinawa yayan yanci
ku yi hakuri banda takaici
duniya ta sai cin hanci
kowa so yake sai ya ci
ana fakewa da rigar yanci
to me ne ne **** yanci
a yau ya zama kacici-kacici
a tsakanin yan bakin ciki
yan yammaci da arewaci
har da na gabashi yan kanci
Safana Feb 2023
Na ga al'amari mai yawa
Daga ciki har da na yawa
Masu aikatawa ne wawa
Ba sa yin komai sai wawa
Da kudin masu cin dawa
Nigeria will decide
Safana Apr 2024
A wanga kasa ta ke nan
Ba a batun wane sai wancan
Komai iyawar ka baka nan
Tun da ba ka cikin yayan nan

Wanga batu lallai zan farawa
Ba kari ciki balle in yi ragawa
Komai nisan jifa kasa zai fadawa
To ko wane ne jifan zai fadawa

Wani jifan tsami wani ko sai zaki
Kafin a jefa jifan sai an sha yaki
Wani yakin tabbas sai an sa kaki
Na gaba-gaba zai nasara shine sarki

A arewa akwai wani birni shine kebbi
In zaka garin zuru lallai sai ka bi
Birni mai tarihi da yawa an bibbi
Malamai da fatake sun fashewar jalabi
Safana Oct 2024
Gona ta
Da na gaje ta
A gurin baban ta
Da babar ta

Kyakkyawa ce
Me haske ce
Me yalwa ce
Da yawan dace

Ciyawa tata ai tsanwa ce
Kai ka ce aljanna ta ce
Don kyawu nata an ce
Mayya ce

Furanni a ciki nata sai kamshi
In na kalla, ido na sai lamshi
In na taba su ko sai laushi
In na shake su zuciya tayi taushi

— The End —