Hello Poetry
Submit your work and get some sparkles! Create free account
In Allah ya yarda za mu yi aure... Mu zauna tare... Dukka hakkokin ki ni zani kare... Mu yo rayuwa bamu ware... Dukka dangi na naki ne babu bare... Zamu zauna a tare... Zani so ki haifa mini jinjiraye yan farare... Rayuwa tana kamshi idan an zauna da mai turare... Ko a kauye zaka ga yara da safe, sun dauko karare... Mata kuwa, a gona tare... suna daukar kirare... Ga iskar damuna tana kadawa har da fure farare... Korama mai sanyin yashi ruwa ya ketare... Ga mu cikin lambu ni da ke mun tattare... Dukka kayan lambu a gaban mu, mun ciccire... Haka ne... In Allah ya yarda Za mu yi Aure... In Allah ya yarda Za mu yi Aure... In Allah ya yarda Za mu yi Aure...
0
Apr 22, 2021
Apr 22, 2021 at 6:59 AM UTC
In Allah ya yarda Za mu yi Aure...

Safana
Written by
33/M/Kano, Nigeria
Apr 22, 2021
Apr 22, 2021 at 6:59 AM UTC
Request permission to use this poem