Hello Poetry
Submit your work and get some sparkles! Create free account
"raini" poems
(ALHAJI (DR.) AMINU ADO BAYERO) Kakkaki Bidigar Sarki Jama'ar birni ku fito... Makasau Dan Bakan Dabo Ya fito. Makasau Sarkin Kano Ya fito Dan Bakan Dabo, Sarki ya fito Aminu Ado, sai da kayi ya fito Saki a kano mai tumbe ya fito Jikan Dabo me ado dan bakan Dabo Makasau sarkin kano mai adon Dabo Me kyautar nera da anini da da kwabo A tarihi nasa an duba kaf babu tabo Ya mike ya tafi al'uma suna ta Odabo Tgwayen sarkin Bichi da kano Fata nasa kowa ya ci a kwano Talawansa su mori dandano Na mulki nasa a bich da Kano Tare da shi a kyakkyawan kwano Jikan Bayero sam baka da raini A cikin dami da sanyi ko ko a rani Jama'a na kaunar ka fanni fanni Saboda kautar nera da anini Da jin kai ga talakawan ka a birni Kirkin ka ya zagawa birni da kauye Ta ko ina alherin ka ya mamaye Gwani, Idan kayi alheri baka waiwaye Saboda a cikin alheri kake a zagaye Hm! makiyan ka kullum za su karairaye Mai hakuri dan mai hakuri, Makasau Ka jure hawan Sallah har zuwa fanisau Akan ingarman dikin ka kamar kosau Wanda babu irin sa ko an je misau Muhammadu Aminu dan Ado Bayero Garnakaki namiji a kyuatar ka ba zero Tsabar ilimin ka turawan sun baka biro Cacnselo a calaba ka wuce a ce Pro Sharrin makiyan k ba ya zuwa ko sun huro dan Bakan Dabo jikan dabo me jalla In ka fito, kwalliyar ka kowa sai ya kalla ana rububin alaka da kai sai an kulla Amma su wancanan ka sai anyi talla Kai! a kano kai kadai ne sarki zalla Kai ka yi kama da Bakan Dabo Ado Mai martaba marigayi sarkin ado Tabbas wannan haka yake kayo gado Tun da ka dare karagar mulkin ka na gado hakika makiyan ka ko sun bi sai sun gudo Ina me ja ya zo ga me tsinkawa Wani ya taba ja mun kai shi takalmawa sai da yayi tattaki ya bi ta wudilawa Ya rtsa gonaki yabi ketaren farawa gashi ta maimaita carki ya tafi ba dwowa Makasau ginshiki ne ga kano da kanawa makasau dirka ne ga kano ba karyewa Makasau Uba ne ga kano ba sauyawa Makasau ka gaji bakan dabo babu adawa Makasau ne sarki daya a kani anyi yabawa
0
Nov 14, 2023
Nov 14, 2023 at 6:20 AM UTC
Makasau Dan Bakan Dabo

Continue reading...
58