Hello Poetry
Submit your work and get some sparkles! Create free account
An share duk wata tantama Lokacin da babu wata Tama Da za'a zuba akan tabarma An fada an nanata fada Babu fada a tskanin fada Ta fada tasa na fada a fada Ga su bature mai jan kunnuwa Ya kifa hula a ka mara kokuwa Cak! ya cake kuma ya rike hannuwa Har da galadima mara hannuwa Ya dunde kai nasa har kunnuwa Kai! kace buzu ne a bisa  ganuwa An tsare tsari can bisa tsauni Sai tsala ihu! ni ku sake ni Ko na dare derere kan tsauni Kaga gada a gada sai yin dara Kallo, kifcen gefe ta ankara Mai harbi da gwafa ta daddara Ka ji biri da dila yan yaudara An ajiye kwalba a cike da madara Sun dauke a guje ba hattara Kai shaho Sarkin dauka na samaniya To ka aje ka gudu ka dau anniya Kar mahari ya hare ka da kibiya
0
Jan 18, 2021
Jan 18, 2021 at 11:27 AM UTC
Traditional Hausa poetry

Safana
Written by
33/M/Kano, Nigeria
Jan 18, 2021
Jan 18, 2021 at 11:27 AM UTC
Request permission to use this poem